Matthew 19

1Sai ya zama sa’adda Yesu ya gama wadannan maganganu, sai ya bar Galili ya zo kan iyakokin Yahudiya, ketaren kogin Urdun. 2Taro mai yawa suka bi shi, ya kuma warkar da su a wurin.

3Farisawa suka zo wurinsa, suna gwada shi, suka ce masa, ‘’Ya hallata bisa ga doka mutum ya saki matarsa don kowanne dalili?‘’ 4Yesu ya amsa ya ce, ‘’Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace?

5Shi wanda ya yi su kuma ya ce, “Saboda wannan dalilin, mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya hade da matarsa, su biyun su zama jiki daya?” 6Su ba biyu ba ne kuma, amma jiki daya. Don haka, duk abin da Allah ya hada, kada wani ya raba.‘’

7Sai suka ce masa, ‘’To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?‘’ 8Sai ya ce masu, ‘’Saboda taurin zuciyarku, shi yasa Musa ya yarda maku ku saki matanku, amma da farko ba haka yake ba. 9Ina gaya maku, duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, yana zina kenan. Wanda kuma ya auri macen da aka saka, yana aikata zina.‘’

10Almajiran suka ce wa Yesu, ‘’Idan haka yake game da mutum da matarsa, ba kyau ayi aure ba.‘’ 11Amma Yesu yace masu, ‘’Ba kowa ne zai karbi wannan koyarwa ba, amma sai wadanda an yardar masu su karbe ta. 12Akwai wadanda aka haife su babanni. Akwai wadanda mutane ne suka maida su babanni. Sa’annan akwai wadanda sun mayar da kansu babanni saboda mulkin sama. Duk wanda zai iya karbar wannan koyarwa, ya karba.‘’

13Sai aka kawo masa yara kanana don ya dibiya hannuwansa akansu, yayi masu addu’a, amma almajiran suka kwabe su. 14Amma Yesu ya ce masu, ‘’Ku bar yara kanana, kada ku hana su zuwa wuri na, domin mulkin sama na irinsu ne.‘’ 15Ya sa hannuwa akan su, sa’annan ya bar wurin.

16Sai wani mutum ya zo wurin Yesu, ya ce, ‘’Malam, wanne ayyuka nagari ne zan yi domin in sami rai madawwami?‘’ 17Yesu ya ce masa, ‘’Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin.‘’

18Mutumin ya ce masa, ‘’Wadanne dokokin?‘’ Yesu ya ce masa, ‘’Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur, 19ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.‘’

20Saurayin nan ya ce masa, ‘’Ai na kiyaye duk wadannan. Me nake bukata kuma?‘’ 21Yesu ya ce masa, ‘’Idan kana so ka zama cikakke, ka tafi ka sayar da mallakarka, ka kuma ba matalauta, zaka sami dukiya a sama. Sa’annan ka zo ka biyo ni.‘’ 22Amma da saurayin nan ya ji abin da Yesu ya fada, ya koma da bakin ciki, domin shi mai arziki ne kwarai.

23Yesu ya ce wa almajiransa, ‘’Hakika ina gaya maku, zai zama da wuya mai arziki ya shiga mulkin sama. 24Ina sake gaya maku, zai fi wa rakumi sauki ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.‘’

25Da almajiran sun ji haka, suka yi mamaki kwarai da gaske, suka ce, ‘’Wanene zai sami ceto?‘’ 26Yesu ya dube su, ya ce, ‘’A wurin mutane wannan ba zai yiwu ba, amma a wurin Allah, kome mai yiwuwa ne.‘’ 27Sai Bitrus ya amsa ya ce masa, ‘’Duba, mun bar kome da kome mun bi ka. To me za mu samu?‘’

28Yesu ya ce masu, ‘’Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari’anta kabilu goma sha biyu na Isra’ila.

29Duk wanda ya bar gidaje, ‘yan’uwa maza, ‘yan’uwa mata, mahaifi, mahaifiya, ‘ya’ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkin su dari, ya kuma gaji rai madawwami. Amma dayawa dake farko yanzu, za su zama na karshe, dayawa dake karshe kuma, su zama na farko.

30

Copyright information for HauULB